
Kwamitin haɗin gwiwa, JAC, na kungiyar ma’aikatan ilimi da hadin gwiwa, NASU, da manyan ma’aikatan jami’o’in Nijeriya, SSANU, sun ce za su janye da yajin aikin da suke yi a ranar Laraba.
Kakakin kwamitin na JAC, Peters Adeyemi, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a jiya Asabar a Abuja.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa, kungiyoyin sun fara yajin aikin ne tun ranar 27 ga watan Maris, domin gaza biyan bukatunsu.
Bukatun ma’aikatan sun hada da yarjejeniyar sake tattaunawa da gwamnatin tarayya ta 2009; rashin tabbas da ya dabaibaye tsari albashi na IPPIS, da maye gurbin tsarin biyan kuɗi tare da Tsarin Biyan Ma’aikata na Jami’a, U3PS, da rashin biyan alawus da aka samu.
Sauran sun haɗa da biyan bashin mafi karancin albashi na kasaa da kuma nazari kan rahotannin kwamiti.