
Jami’an tsaron farin kaya da na tsaron gidan yarin sun gabza a kan tafiya da dakataccen gwamnan Babban Bankin Kasa, CBN, Godwin Emefiele s yau Talata.
Ofishin Antoni Janar ne ya gurfanar da Emefiele, karkashin ma’aikatar shari’a.
An gurfanar da shi ne da misalin karfe 9:21 na safiyar yau, a gaban mai shari’a Nicholas Oweibo, bisa tuhumarsa da laifuka biyu na mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.
Ya musanta laifin da ake tuhumarsa da shi, kuma an bada belinsa a kan kudi naira miliyan 20.
Kotun ta ɗage ci gaba da sauraron karar har sai ranar 14 ga watan Nuwamba, sannan ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake kara a gidan gyaran hali har sai an kammala belinsa.
Bayan an dage sauraron shari’ar, sai Emefiele ya ci gaba da zama a harabar kotun na sa’o’i da dama.
Ƴan jarida da su ke kotun sun tattaro cewa duk lokacin da suke jira a harabar kotun, jikin su ya basu cewa da wuya DSS ba su sake kama wanda Emefiele ba, bayan da su ka ga jami’ansu dauke da makamai a kotun
A lokacin da jami’an gidan yarin suka kai Mista Emefiele a gidan yari har sai an cika sharuddan belinsa, ‘yan sandan farin kaya sun kalubalanci su, lamarin da ya haifar da cece-kuce a kusa da kotun.
A wani faifan bidiyo da ke yawo a yanar gizo, an ga yadda aka yaga kakin wani jami’in gidan yari da ake zargin jami’an SSS ne su ka doke shi.
Wasu lauyoyi da ƴan kallo da ke harabar kotun, sun yi tir da rashin da’a na ‘yan sandan sirri, inda suka rika rera taken: “Abin kunya gs DSS, DSS ta ji kunya”.
Duk hukumomin biyu har yanzu ba su mayar da martani ga faifan bidiyon ba har zuwa lokacin wallafa da wannan rahoto.