Home Labarai SSS sun sake damƙe Emiefele awanni kaɗan bayan kotu ta bada belin sa

SSS sun sake damƙe Emiefele awanni kaɗan bayan kotu ta bada belin sa

0
SSS sun sake damƙe Emiefele awanni kaɗan bayan kotu ta bada belin sa

Hukumar tsaron farin kaya, SSS, ta sake kama tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele, jim kadan bayan wata babbar kotun tarayya da ke Legas ta bayar da belinsa.

Ofishin Antoni Janar ne ya gurfanar da Emefiele, karkashin ma’aikatar shari’a.

An gurfanar da shi ne da misalin karfe 9:21 na safiyar yau, a gaban mai shari’a Nicholas Oweibo, bisa tuhumarsa da laifuka biyu na mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.

Ya musanta laifin da ake tuhumarsa da shi, kuma an bada belinsa a kan kudi naira miliyan 20.

Kotun ta ɗage ci gaba da sauraron karar har sai ranar 14 ga watan Nuwamba, sannan ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake kara a gidan gyaran hali har sai an kammala belinsa.

Bayan an dage sauraron shari’ar, sai Emefiele ya ci gaba da zama a harabar kotun na sa’o’i da dama.

Ƴan jarida da su ke kotun sun tattaro cewa duk lokacin da suke jira a harabar kotun, jikin su ya basu cewa da wuya DSS ba su sake kama wanda Emefiele ba, bayan da su ka ga jami’ansu dauke da makamai a kotun.

A lokacin da wani babban jami’in hukumar gyaran hali ta Najeriya, NCoS, ya yi yunkurin kai wanda Emefiele zuwa gidan yari bisa ga umarnin kotu, wanda ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare shi har sai an kammala beli, hukumar DSS ta bijirewa matakin.

Bayan wata arangama tsakanin jami’an SSS da na NCoS, daga karshe jami’an SSS sun samu nasarar tafiya da Emefiele a lokacin da ya fito daga dakin kotun, inda suka tafi da shi cikin motar ƴansanda da misalin karfe 3:15 na rana.

Ba a dai bayyana dalilin da ya sa jami’an SS suka tafi da tsohon gwamnan na CBN ba