
Daga Abubakar Aminu Ibrahim
Bai zamo abin mamaki ba yadda ‘yan adawa sukeson ganin bayan Gwamnatin Ganduje ta APC a jihar KANO, ganin irin yadda al’ummar jihar kano suka tsaya kai da fata wajen biyayya ga gwamnatin datake qaunarsu ta Mai girma Abdullahi Umar Ganduje da Baba Buhari.
A zahirin gaskiya dole ne hankalin ‘yan adawa ya tashi tun daga lokacin da akace Baba Buhari da shi kansa Gwamna Ganduje sun samu ‘kuri’u kimanin miliyan biyu da ‘doriya, hakan ya harzuqo ma’kiya kuma yatashi hankali su, wanda ya sanya suke neman duk wata hanya da zasu bawa wannan gwamnatin matsala, wannan shine ummul aba’isin kawo wani faifan bidiyo don a’bata sunan Mai girma Gwamna Ganduje.
Azahiri kowa yasan duk arewacin Nijeriya babu inda suke qaunar Shugaba Buhari kamar KANO, babu inda suke bawa Shugaban ruwan ‘kuri’u kamar kano, a siyasance duk wanda yaci KANO a arewacin kasar dake da jihohi 19, to babu ko tantama shine ya cinye za’ben kasar. Sannan a duk arewacin kasar babu inda ‘yan adawa suke bukatar kassara kuri’un Shugaba Buhari kamar Kano, wanda ta sanya sukeson su lalata mutincin da Gwamna Ganduje yake dashi, da kuma hada jam’iyyar APC da al’ummar jihar KANO masu mutunci, wanda suke ganin idan har APC suka rasa kuri’un jihar kano to tamkar sun karya lagon Shugaba Buhari ne.
Sannan ‘yan adawar mu na Kano a yanzu sunga basu ga tsuntsu basu ga tarko, dimbin ayyukan da Gwamna Ganduje yakewa kanawa, qauna da soyayya da al’ummar jihar KANO sukewa Gwamna, hakan yatashi hankalinsu da sun rasa madafa, hakan ya sanya suka ‘kir’kiri wata hanya ta lalata mutincin Gwamna, wannan ta sanya suka ‘kir’kiri bidiyon da zasu lalata dattijantaka ta Gwamna da cewar yana amsar na goro daga hannun ‘yan kwangilar sa.
Ta Allah bataku ba ‘yan adawa, kunci lokacin ku kubar wasu suci lokacin su. A fili take kuma azahiri shi wanda yake ikirarin wannan fayafayan bidiyon har kawo yanzu yakasa saki, saboda asirin sa ya tonu, mun tabbatar da wa yakewa aiki, munsan suwaye suke sashi…
Muna kira da al’ummar jihar KANO da kar su dauki wata jita-jita, sannan suyi kunnen uwar shegu da duk wata kafa da take bada ra’ifin labari don aci mutincin Shugabanni. Sannan suci gabada biyayya ga Gwamnatin jihar kano data Baba Buhari don ci gabada more romon dimokrdiya.
Abubakar Aminu Ibrahim Babban Mataimakin Gwamna akan Sabbin Kafafan yada Labarai.