
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ƙalubalanci mambobin kwamitin yaƙin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, ɓangaren mata da su yi aiki tukuru domin ganin jam’iyyar ta samu nasara a zaben 2023 mai zuwa.
Shugaban, wanda ya yi wannan kira a wajen ƙaddamar da kwamitin mata na jam’iyyar APC a Abuja a jiya Litinin, ya ce kiran ya zama wajibi duba da yadda babu wani zaɓi sama da APC a zaben shugaban kasa na 2023.
Buhari, wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Farfesa Ibrahim Gambari ya buƙaci matan da su ba dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Bola Tinubu da kuma mataimakinsa, Kashim Shettima goyon baya kamar sauran ‘yan takarar jam’iyyar APC a lokacin zabukan 2023 da kuma bayan zaben.
Ya bayyana kaddamar da kwamitin yakin neman zaben mata na jam’iyyar APC a matsayin muhimmin bangaren yakin neman zaben 2023.
“Don haka ina kira ga daukacin mambobin wannan kwamiti da su dauki wannan gagarumin nauyi a matsayin shaida na sadaukar da kai ga jam’iyyar APC.
“Ina da yakinin cewa wannan kwamiti zai kai jam’iyyar APC zuwa ga kololuwa ta hanyar bullo da aiwatar da dabarun jam’iyya baki daya don tabbatar da nasarar zaben 2023, domin babu wata hanyar da ta wuce nasararmu,” inji shi.