
Bankin da baya ta’ammali da kuɗin ruwa, TAJBank ya zama shine gwarzon bankin musulunci na shekara.
Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa TAJBank ya lashe kyautar ne a wani bikin bada kyaututtuka na shekara ga bankuna da sauran ma’aikatun harkar kuɗaɗe, BAFI 2021, da jairdar BusinessDay ta gudanar.
Wannan kyautar ta zo ne watanni biyu bayan da bankin ya lashe kyautar gwarzon shekara da jaridar Leadership ta gudanar.
Mahukunta a kamfanin BusinessDay, a wata sanarwar da su ka fitar, sun ce TAJBank ya lashe kyautar ne sakamakon ƙir-ƙire na harkar banki da yanke yi da kuma yadda ya ke daɗaɗawa abokan sa hulɗarsa.
Sanarwar ta ce” TAJBank ya bada mamaki a harkar banki bayan kafa shi a 2019.
“Yadda bankin ya kawo sauyi mai kyau da kuma ƙirƙire-ƙirƙire da wasu tsare-tsare ma zamani da kuma yadda ya ke bunƙasa harkar kuɗaɗe da daɗaɗawa abokan hulɗa, ya bada mamaki ƙwarai,”
Mahukuntan kuma sun yi hasashen cewa nan da 2021 zuwa 2026, harkar bankin musulunci za ta samu bunƙasa da kaso 15 cikin ɗari.
Jaridar ta kara da cewa in dai TAJBank ya sami lasisin yin harkar banki na ƙasa, to zai ƙara bunƙasa da kashi 65 cikin 100.
Da ya ke bayani bayan bada lambar girman, shugaban TAJBank, Hamid Joɗa ya nuna cewa nasarar ta nuna cewa lallai bankin ma kan hanyarsa ta ƙoƙarin bunƙasa harkar banki maras ruwa a Nijeriya.