
Daga Hassan Malik
Maitaimaki na musamman ga shugaba Muhammadu Buhari kan harkokin siyasa, Babafemi Ojudu ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamna a jiharsa ta Ekiti a karkashin inuwar jam’iyara APC.
Jam’iyyar adawa ta PDP a jiya Juma’a ta shawarci gwamnatin tarayya da ta kori ministanayyukan noma, Cif Audu Ogbeh bisa abinda ta kira sanya a Nijeriya a bakin duniya a matsayin makaryaciyar kasa. PDP ta bayayana cewa duniya ta girgiza matuka bayan da jakadan kasar Thailand a Nijeriya ya fito ya karyata batun da Ogbeh ya yi na cewa kasar Thailand na ta rufe kamfanonin sarrafa shinkafarta saboda Nijeriya ta daina shigo da shinkafa daga can.
Jam’iyyar APC ta shawaraci reshenta na jihar Legas da ta dakata har zuwa lokacin da jam’iyyar za ta sake gudanar da babban taronta na kasa sannan sai ta bayyana rashin amincewarta da zarcewar da shugabannin jam’iyyar ta kasa suka yi akan mukamansu.
Wani rahoto ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta kaddamar da tallafin Naira dubu biyar-biyar ga mutane 10,623 a kananan hukumomi 9 na jihar Kaduna.
Shugaban jam’iyyar APC na jihar Ribas, Cif Davies Ikanya ya gargadi gwamnan jihar, Nyesom Wike cewa ya guji ya dada kalaman tunzuri a fadin jihar tun bayan samun labarin cewa shugaban Buhari zai kai ziyarar aiki jihar.
Babbar kotun gwamnatin tarayya da ke zamanata a jihar Legas ta samu bayani daga majiya mai tushe cewa tsohuwar ministar harkokin man fetur ta kasa, Diezani Alison-Madueke ta karbi kudi har dalar Amurka miliyan 115.01 daidai da Naira biliyan 23 daga wajen ‘yan kasuwar man fetur guda 3, gabanin zaben 2015, kuma ta rarraba kudaden ga wasu masu ruwa da tsaki na jam’iyyara PDP.
Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaro masu lura da gwamnan jihar Neja, Sani Bello, a ranar Alhamis din da ta gabata sun bude wuta akan matasa sakamakon ihun “Sau Daya” da “Bama Yi” da suke ta yi wa gwamnan a lokacin da ya shiga garin Bida don duba kasuwar da ta yi Gobara. Bidiyon abunda ya wakana a bayyana a kafafafen yada labarai a jiya Juma’a.
Dan uwan shugaban kungiyar fafutukar kafa yankin Biafra ta IPOB, Prince Emmanuel Kanu, a zargi shugaban kungiyar MASSOB, Ralph Uwazuruike bisa sac yayansa, Nnamdi Kanu, tare kuma da mika shi ga sojojim Nijeriya.
Rahotanni sun bayyana cewa, kasa da awanni 24 da kaddamar da wata taswirar zaman lafiya ta shekaru 5 tsakanin fulani makiyaya da manoma a jihar Filato da shugaba Muhammadu Buhari ya yi, sai kwatsam fulani makiyaya suka kai farmaki akan garin Nzharuvo cikin karamar hukumar Bassa. Rahoton ya bayyana cewa mutane akalla guda 15 ne suka rasa rayukansu a harin na dare Alhamis.
Allah ya takaita hatsarin jirgin saman kamfanin Arik bayan da matuka jirgin suka fahimci cewa hayaki na fita daga cikin jirgin (inda matuka jirgin ke zaune). Jirgin mai lamba W3304 ya yi saukar gaggawa.