Home Labarai Ɗan takara ɗaya ne tak ya zo wajen mu gwaji a Katsina — NDLEA

Ɗan takara ɗaya ne tak ya zo wajen mu gwaji a Katsina — NDLEA

0
Ɗan takara ɗaya ne tak ya zo wajen mu gwaji a Katsina — NDLEA

 

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, ta ce ɗan takara ɗaya ne tak a dukkanin jam’iyyun siyasar da ke neman mukamai daban-daban ya zo domin yin gwajin a jihar Katsina.

Kwamandan NDLEA a jihar, Muhammed Bashir ne ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labarai na ƙasa a jiya Talata a Katsina.

A cewarsa, ɗan takarar gwamna na jam’iyyar People’s Redemption Party, PRP, Imran Jino ne kaɗai ya ziyarci hukumar domin gwajin, ya kara da cewa kyauta a ka yi masa gwajin.

Ya kuma buƙaci ƴan siyasa da ke neman mukamai daban-daban a jihar da su zo domin yin wannan gwaji, yana mai cewa hakan zai zama saƙo ga magoya bayansu.

Kwamandan na NDLEA ya kara da cewa yin haka da ƴan siyasan ke yi zai karfafa wa magoya bayansu kwarin guiwa su guji shaye-shayen miyagun kwayoyi.