Home Siyasa Ɗan takara ɗaya ne ya ƙi yarda da sasantawa a APC sai idan shi aka zaɓa — Oyegun

Ɗan takara ɗaya ne ya ƙi yarda da sasantawa a APC sai idan shi aka zaɓa — Oyegun

0
Ɗan takara ɗaya ne ya ƙi yarda da sasantawa a APC sai idan shi aka zaɓa — Oyegun

 

 

Shugaban kwamatin tantance ‘yan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, John Oyegun, ya ce kashi 99 cikin 100 na masu neman takarar sun amince su goyi bayan ɗan takara ta hanyar sasantawa ban da ɗan takara kacal.

Mista Oyegun ya faɗi hakan ne lokacin da yake gabatar wa shugaban APC Abdullahi Adamu rahoton kwamatin nasa a ranar Juma’a.

“Mun tattauna da dukkan masu neman takarar game da sasantawa,” a cewarsa. “Abin mamaki kashi 99 cikin 100 sun amince cewa jam’iyyar ce gaba da kowa kuma duk abin da ta yanke – ta hanyar cikakkiyar tuntuɓa – akwai yiwuwar su amince.

“Mutum ɗaya ne kawai ya ce zai yarda da sasantawa amma sai idan shi aka zaɓa. Ina ganin abu ne da ya kamata a faɗa kuma a sake maimaitawa.

“Saboda haka wannan dama ce da muka samu ta sake rage yawan ‘yan takarar sosai. Amma daga ƙarshe ina ganin bai kamata mu ji tsoron gudanar da zaɓe ba idan wani ɗan takara ya haƙiƙance a kan hakan.”

Kwamatin ya rage yawan ‘yan takarar daga 23 zuwa 10 yayin tantancewar da aka gudanar a farkon makon nan.