
Ɗan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a Jihar Bauchi, Ibrahim Kashim, ya janye daga takarar.
DAILY NIGERIAN ta samo bayanai cewa Kashim ya bar wa gwamna Bala Mohammed takarar ne, bayan da ya sha kaye a zaɓen fidda-gwani na shugaban kasa na jam’iyyar PDP.
Kakakin jam’iyyar, Yayanuwa Zainabari, ya shaida wa taron manema labarai a Bauchi a jiya Talata cewa Kashim ya janye daga takarar ne bisa dalilai na ƙashin kansa.
Ya ce nan ba da jimawa ba PDP za ta bi tsarin da ya dace domin maye gurbin Kashim ɗin da wani.
“Za mu bayyana matsayinmu a cikin wannan makon.
“Zabin da ya rage wa jam’iyyar shi ne ta mika sunan wanda zai maye gurbinsa ga INEC domin cika ƙa’idoji ,” in ji shi.