
Dan takarar gwamna a jam’iyar PDP a Jihar Plateau, Caleb Mutfwang, a yau Talata a Jos ya zaɓi Josephine Piyo a matsayin mataimakiyarsa a takarar zaɓen 2023.
Mutfwang ya ce matakin da ya ɗauka na zaɓar Piyo abu ne mai wahala duba da irin ɗumbin mutanen da su ka cancanta a zaɓa.
“A yayin yanke wannan shawarar, na yi shawarwari ma su zurfi da shugabannin jam’iyyarmu, da masu ruwa da tsaki daban-daban kafin na zabi abokiyar takarara don inganta tikitin hadin gwiwa na shiga babban zabe.
“Wasu daga cikinku za su tuna cewa a lokacin yaƙin neman zaɓe na gabanin zaɓen fidda-gwani na jam’iyyar, na yi alƙawarin tallafa wa mai ƙaramin ƙarfi.
“Dole ne na fito fili na bayyana cewa wani ɓangare mai mahimmanci na al’ummarmu da aka yi watsi da shi a cikin la’akari da shugabanci shine mata amma duk da haka suna samar da kaso mai tsoka na yawan al’ummarmu.
“A gare ni, ba su murya ya zama dole,” in ji shi.
Dan takarar gwamnan ya bayyana Piyo wacce ta fito daga karamar hukumar Barkin Ladi a jihar a matsayin ƴar siyasa kuma mace mai biyayya.