
Ɗan takarar kujerar majalisar wakilai ta mazaɓar Kananan Hukumomin Kiru da Bebeji, Abdulmumin Jibrin Kofa, ya karɓi mutane sama da 2,000 da su ka sauya sheƙa daga jam’iyyu daban-daban a yankin nasa.
Kofa ya karɓe su ne a jiya Litinin a taron ƙaddamar da fara yaƙin neman zaɓen sa, wanda a ka yi a garin na Kofa.
Taron ya samu halartar dubban magoya baya daga Kananan Hukumomin Kiru da Bebeji.
Yayin taron, waɗanda su ka koma jam’iyyar NNPP ɗin sun yi alakwarin aiki tukuru wajen baiwa dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar, Rabiu Musa Kwankwaso kuri’a miliyan 5 da kuma ganin jam’iyyar tayi nasara tun daga sama har kasa.
A yayin taron, Kofa ya yi alkawarin idan ya ci zaɓe, zai ci gaba da kawo ayyukan ci gaba kamar yadda ya saba a mazaɓar ta sa.
Taron ya samu halartar ƴan takarar majalissar jiha na Kiru Hon Abubakar Usman Rabula Dana Bebeji Hon Ali Muhammed Tiga da dai sauran yan jam’iyya.