
Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta bayyana dan takarar jam’iyyar PDP, Ademola Adeleke, a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna na Jihar Osun.
Da yake bayyana sakamakon zaɓen da safiyar Lahadi nan, babban jami’in zaɓe na INEC a jihar Osun, Oluwatoyin Ogundipe, ya ce ɗan takarar PDP ɗin ya lashe zaɓen ne bayan da ya samu ƙuri’u 403,371.
Ogundipe ya ce Gboyega Oyetola, gwamna mai ci kuma ɗan takarar jam’iyyar APC, ya samu ƙuri’u 375,027, inda ya zo na biyu.
Ya ce ɗan takarar PDP ya cika dukkan sharuɗɗan doka, kuma “an bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara kuma ya zama zaɓaɓɓen gwamna.”
Adeleke ya lashe ƙananan hukumomi 17 cikin 30 na jihar.
Zaɓen gwamnan jihar Osun na shekarar 2022 an gudanar da shi ne a dukkanin ƙananan hukumomin jihar 30 da ke da rumfunan zabe 3,763 da kuma wuraren rajista 332.