Home Siyasa Ƴan takarar shugaban ƙasa 7 sun yi wancakali da sunayen da gwamnonin APC su ka miƙa wa Buhari

Ƴan takarar shugaban ƙasa 7 sun yi wancakali da sunayen da gwamnonin APC su ka miƙa wa Buhari

0
Ƴan takarar shugaban ƙasa 7 sun yi wancakali da sunayen da gwamnonin APC su ka miƙa wa Buhari

 

 

 

Ƴan takarar shugaban kasa su bakwai, a ƙarƙashin jam’iyyar APC, sun yi wancakali da sunayen wasu ‘yan takarar shugaban kasa biyar da aka ce an aike wa shugaban kasa Muhammadu Buhari domin ya zaɓi dan takara na maslaha a cikinsu.

Masu neman takarar, a cikin wata sanarwa da suka fitar da sanyin safiyar Talata, jim kadan bayan wani dan takaitaccen taron da suka yi a Abuja, masu neman takarar sun barranta kansu daga jerin sunayen da aka ce an miƙa wa Buhari.

Ƴan takarar , da su ka haɗa da gwamnan jihar Cross River, Ben Ayade; tsohon karamin ministan ilimi, Emeka Nwajiuba; Tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu, tsohon Gwamna Rochas Okorocha da hamshakin dan kasuwa Tein Jack-Rich, sun jaddada cewa ba a tuntube su ba kafin gwamnonin su kai ga yanke shawara.

Bayan da su ka bayyana matakin a matsayin abin kunya da kuma yunkurin ganin bayan wasu masu son tsayawa takara, musamman na yankin Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu, masu neman takarar sun nuna goyon bayansu ga shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Adamu.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “A cikin ƴan sa’o’i da suka gabata an yi ta fama da kiraye-kiraye da sakonni daga magoya baya da kuma ƴan Najeriya da suka damu, a cikin jerin sunayen ‘yan takarar shugaban kasa biyar da aka mika wa shugaba Buhari domin ya zaba daga cikinsu.

“Matukar dai babu wani jerin sunayen da aka mika wa Maigirma shugaban kasa, matakin da gwamnonin suka dauka ana daukarsu tamkar wasa ne da nufin wasa da hankalin ƴan Nijeriya, musamman mu daga Kudu maso Gabas.

“Umarnin Shugaban kasa abu ne mai sauki, cewa duk masu neman Shugaban kasa har da na Arewa su hadu su daidaita domin a samar da dan takara daya. A halin da ake ciki ba a tuntube mu ko halartar wani taro ba inda aka amince a aika wa shugaban kasa irin wadannan sunaye.

“A cikin jerin sunayen da aka kira a cikin sunayen biyar, ɗaya ne kawai aka zaɓa daga Kudu maso Gabas kuma muna magana ne akan adalci da adalci ga Kudu.