Home Siyasa Takarar shugabancin ƙasa ta 2023: An kammala tantance Osinbajo

Takarar shugabancin ƙasa ta 2023: An kammala tantance Osinbajo

0
Takarar shugabancin ƙasa ta 2023: An kammala tantance Osinbajo

 

 

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya samu nasarar tantancewa da kwamitin tantance ƴan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ke gudanar wa.

Osinbajo ya zanta da manema labarai jim kadan bayan fitowa daga ɗakin tantancewar da aka gudanar yau Talata a otal ɗin Transcorp Hilton da ke Abuja.

Mataimakin shugaban kasar ya ce aikin ya yi matukar tasiri tare da bayyana kwarin guiwarsa na jan ragamar jam’iyyar a zaben shugaban kasa na 2023.

“Mun tattauna batutuwa da dama; batutuwan da suka shafi kasa da jam’iyya; kuma maganganun namu masu ma’ana ne; mun yi hira sosai.

“Tabbas muna gaban kowace jam’iyya APC na gaba a ƙasar nan,” inji shi

Kwamitin da Cif John Odigie-Oyegun ke jagoranta, wanda ya fara aiki a jiya Litinin, zai tantance a ƙalla ƴan takara 25 masu neman tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC.