
Jagoran Majalisar Dattawa, Yahaya Abdullahi, a jiya Juma’a ya baiyana cewa ya fice daga jam’iyyar APC ne saboda “rashin adalci” a reshen jam’iyar na Jihar Kebbi.
A ranar Laraba ne dai Abdullahi, mai wakiltar Kebbi ta Arewa ya koma jam’iyyar adawa ta PDP a jihar.
Dan majalisar ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN a Abuja cewa “magana ce ta tauye hakki”.
Ya ce: “Eh, na bar APC ne saboda rashin adalci da ga Gwamnan Jihar Kebbi.
“Ba zalunci ba ne kawai; tauye haƙƙoƙi ne da rashin bin dimokuraɗiyya wanda mu ka kai rahoto ga jam’iyyar fiye da watanni 11.
“Ba wanda ya yi wani abu game da yadda gwamnan ke tafiyar da harkokin jam’iyya a jihar; ƙaƙaba ƴan takara da yin duk abin da ya ga dama.
“Shelkwatar jam’iyyar ta kasa ta kasa ta ƙi ta sa baki. Mu kuma ba za mu zauna kawai mu ajiye tamu buƙatar don ci gaban harkokin siyasa da ci gaban wani mutum ɗaya ba.
“Mun yi tunanin abin da ya fi dacewa shi ne mu bar jam’iyyar,” in ji Abdullahi.
NAN ta rawaito cewa sauya shekar Abdullahi bazai rasa nasaba da rasa tikitin takarar gwamnan APC a ranar 26 ga watan Mayu ba.