
Sani Buba, Shugaban Kwamitin Tallafi na Jihar Borno, a yau Alhamis ya tabbatar da kama mutane 26 bisa zargin karɓar rashawa a hannun mata ƴan gudun hijira da s ka yi wa rijista a cikin shirin tallafin.
Buba ya bayyana haka ne yayin da ya ke bibiyar ci gaban da s ke samu a rabon kayan abinci da wanda ba na abinci ba ga gidaje dubu 100 a Ƙananan Hukumomin Maiduguri da Jere.
Ya ce matan ne su ka miƙa ƙorafin su zuwa ga kwamitin, inda shi kuma kwamitin ya miƙa shi ga ƴan sanda.
Buba ya ƙara da cewa ƴan sandan sun kame mutane 26 da s ke zargi kuma ana ci gaba da bincike.
Ya kuma yaba wa matan bisa ƙorafin da su ka kai, inda ya yi kira ga sauran mata da su rika mika korafi idan sun ga ana yin badaƙala a cikin shirin zuwa ga hukumomin da su ka dace.