
Da ga Salisu Ismail Kabuga
Tabbas idan ka ji korafi akwai rashin gamsuwa, kamar yadda indai ka ji tambaya akwai abinda ya shigewa mutum duhu.
Assalamu Alaika Ya Shugaba Muhammad Buhari. Shugaban Najeriya.
Duba da ya yanayin yadda lamarin tsaro da sauran harkokin rayuwa, wadan da sai da rai da lafiya ake batunsu suka kara tabarbarewa a Najeriya, Musamman Arewa, yadda batun ta’addanci da zulumin kai farmaki a garuruwa da hanyoyi, da wajajen noma ko wajajen neman halak (Kasuwanni) suka kara jefa rayuwar takala cikin kunci, Sune dalilan rubuta wannan Wasika “Kai-Tsaye” cikin girmamawa gare ka.
Abinda ya sa wannan wasika ta zama “kai-Tsaye” kuma da sigar tambaya gare Ka ya Shugaban Najeriya Muhamnadu Buhari shine, Mu dai a Muslinci munkwana da sanin cewa akwai abinda aka yadda wani zai iyayi a madadin wani, Yayin da wani lamarin kuma kowa sai dai yayiwa kansa, Ma’ana wani baya wakiltar wani.
Haka kuma, su kansu a abubuwan da ake iya bada wakilcin matukar akwai abinda ya shiga duhu tsakanin wanda aka aikawa wakilin da kuma wakilin, akwai damar tafiya kai tsaye zuwa ga wanda ya bada wakilcin, wannan shine dalilin neman wannan amsar daga gare ka Shugaban mu, Muhammadu Buhari domin kaine wanda al’umar Najeriya muka dankawa amanar jagorancin mu.
Mai Girma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ka san cewa dukkannin dan’adam gajiyayye ne kuma ajizi ne- ya kan daɗa himma ko ya rage a al’amuran rayuwa.
Hakan ya sa amsa wadannan (TAMBAYOYI GUDA 10) da kanka na ke da yakinin ko ba komai wata hanyace da za ka san matsayin da ka ke, wanda mu kuma ƴan Nijeriya muma zamu fa’idantu wajen ganin sauyi a zahiri, yayin da Allah ya baka ikon amsawa kanka da kanka wadannan TAMBAYOYI wadanda ba sa bukatar wakilcin wani mukarrabin ka.
Ga Tambayoyin daya-bayan-daya, wadanda Allah yasa ni ban yi su da kudurin izgili ko wata manufa ba, face na ganin al’amuran kasa sun gyaru, wadan da kuma na ke fatan zasu samu duba na tsanaki.
{1} Ya Shugaba Muhammadu Buhari, anya kuwa ka na iya tuna yadda a baya kafin mu zabe ka, ka dinga kushe shugabannin baya saboda abinda mu da kai mu ka yadda sakaci ne wajen iya jagorancin ƴan Najeriya ?
{2} Anya kuwa Kana tuna yadda ka dinga bibiyar ƴan Najeriya domin mu yarda za ka iya share mana hawaye, har mu ka aminta mu ka baka amanar kanmu da ta rayuka da dukiyoyin mu da hakkin kare mutuncin mu a 2015 ?
{3} Anya kuwa ka na iya tuna rahotannin yadda tsaffi masu shekaru da yawa (Old-ages) da mata masu juna biyu (pregnant women) da yadda wadansu daga cikin wadan da ke jinya a Glgida dana asibitoci su ka rarrafa suka je suka wuni a layin zabe cikin ƙishurwa da yunwa da zafin rana domin zabar ka ?
{4} Anya kuwa Kana iya tuna yadda ƴan Najeriya (Talakawa) su ka ki ci, su ka ki sha, su ka dinga kankare kati domin aika maka da tallafin kudi domin ka kai ga nasara a zaben 2015 ?
{5} Anya kuwa ka na iya tuna yadda rashin lafiya, wadda tana kan kowa, ta same ka jin kadan bayan an zabe ka. Talakawan da su ka zabe ka su ka kasa zaune su ka kasa tsaye a gidajensu da makarantunsu da masallatai da majalisu dare da rana su ka dinga yi maka addu’a domin ka samu lafiya ka futar dasu daga takaici ?
{6} Anya kuwa Shugaba Buhari a matsayin ka na Musulmi ka na iya tuna kalaman dake cikin rantsuwar kama mulki da ka saɓa lokutan rantsar da kai a Abuja da sauran jawaban da kayi a ranar?
{7} Shin Shugaba Buhari ka ma yarda cewa Najeriya da ƴan Najeriya, musamman talakan Arewa na cikin mawuyacin hali da zullimin tsaro ?
{8} Ya Shugaba Muhammadu Buhari, shin ka san cewa yin tattaki domin jajantawa da yin sannu, hadi da addu’a ga wanda ke cikin damuwa koda bazai samu waraka ba abune mai dadi ga wanda ke cikin irin wannan hali? Kamar yadda sanda ka kwanta rashin lafiya a Landan, talakawan ka sukai ta yi maka addu’a, harda yin yanka da bada sadaqa.
Wanda na san a lokacin, in da a ce Birnin Landan kamar nisan Jakara zuwa Gauron Dutse ya ke, da duk da baza’a basu damar ganin ka ba, dasun yi dafifi a garin da kake jinya domin nuna alhini, amma kai gashi gari ya gari, jirgi kawai zaka hawo ka jajantawa Katsinawa da Sokkwatawa da sauran gururuwan Arewa, amma abin ya faskara.
{9} Har ila yau, Anya kuwa Buhari a matsayin ka na Musulmi ,wanda ya samu tarbiyyar kasar Hausa, ka yi makarantar addini kamar yadda duk Musulmi ke yi, ka yarda cewa akwai hisabi bayan mutuwa, kuma cikin hisabin za’a tambayeka duk abinda ka yi da ma wanda ka ki yi, wanda a dalilin hakan rayuwar mutane da mutuncin su ke salwanta ?
{10} Shin sai a wanne lokacin ne Shugaba Buhari ka ke zatan alkawura da kuma kyawawan kudurori da ka zawarci kuri’un ƴan Najeriya sa zu cika? In kuma kai kanka ka yanke kauna, abin yafi karfin ka, to yaushe za ka yiwa ƴan Najeriya bayani kai tsaye saboda musan mataki na gaba ?
Wadannan suke jerin tambayoyi, ko kuma ka kalle su a matsayin tuhumar da indai Allah Ya baka iko ka iya amsawa kan ka da kan ka su, kuma ka dauki matakin da ya dace yanzu-yanzu, to kuwa nan take muma zamu ji amsar a jikin mu da kuma ganin amsar da idan mu, domin amsar tambayoyin kamar yadda na ce a aikace ƴan Najeriya zamu gani.
Allah ya baka ikon dubawa da daukar matakin da ya dace a kan lokaci.
Ko wanne ɗan kasa da iyakacin aikin da hurumin kundin mulki ya sahale masa. Wannan shine nawa hurumin a matsayi na na dan jarida mai fatan ganin kasa ta, Najeriya ta kyautatu.
Comrade Salisu Ismail Kabuga ya rubuto da ga Jihar Kano kuma za a iya tuntuɓar sa a kan:
salkabuga@gmail.com
+2348052529040
12/12/2021