Home Labarai Tambuwal ya tabbatar da kisan mutane 43 a Illela

Tambuwal ya tabbatar da kisan mutane 43 a Illela

0
Tambuwal ya tabbatar da kisan mutane 43 a Illela

 

Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya tabbatar da kisan mutane 43 a harin da ƴan ta’adda su ka kai a Ƙaramar Hukumar Illela.
Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwar da kakakin gwamnan, Muhammad Bello ya fitar a yau Alhamis a Sokoto.
Bello ya ce gwamnan ya jagoranci jami’an gwamnati da na tsaro da sauran ma su ruwa da tsaki zuwa ta’aziya ga al’ummar garin Illela a ranar Laraba.
Illela na da nisan kilomita 97 daga cikin garin Sokoto, inda ƙaramar hukumar ke fama da harin ƴan ta’adda a ƴan kwanakin nan.
A cewar sanarwar, ƴan ta’addan sun kai hari garin ne da sauran ƙauyukan da ke maƙwabta da tsakar dare in da su ka hallaka mutane 13 a ranar 15 ga watan Nuwamba.
Bello ya ƙara da cewa Tambuwal ya nuna alhini da baƙin-ciki game da ibtila’in da ya faɗawa al’ummar garin, inda ya yi alƙawarin cewa gwamnatin sa za ta samar da wata runduna ta haɗin-gwiwa da jami’an tsaro domin samar da zaman lafiya a yankin.
Ya kuma yabawa jami’an tsaro da ƴan vigilante na yankin a bisa namijin ƙoƙarin da su ke yi wajen yaƙi da ƴan ta’addar.