
A yau Litinin ne Babban jami’in kula da Harkokin Waje na Tarayyar Turai, EU, Josep Borrell, ya ce kamata ya yi ƙungiyar ta ɗauki matakin karɓe asusun Russia na kuɗaɗen waje don taimakawa wajensake gina Ukraine bayan yaƙin da su ke yi a yanzu.
A wata hira da jaridar Financial Times, Borrell ya ce EU da ƙawayenta na yammacin Turai sun sanya takunkumi kan asusun ajiyar babban bankin Russia na ƙasa da ƙasa tun lokacin da ƙasar ta fara mamaye Ukraine.
Ya ce zai yi ma’ana ga EU ta yi abin da Amurka ta yi da kadarorin babban bankin Afganistan bayan ‘yan Taliban sun mamayen kasar ta Asiya.
“Muna da kuɗin a cikin aljihunmu, kuma ya kamata a bayyana menene dalilin da ya sa a ka karɓe kuɗaɗen Afganistan kuma bai dace a karɓe kudin Russia ba,” in ji Mista Borrell.
Washington ta rufe asusun kudaden Afganistan bayan da sojoji su ka karɓe iko da Taliban tare da shirin yin amfani da wasu don taimakawa al’ummar Afganistan tare da rike sauran don shari’o’i da ke da alaka da ta’addanci a kan masu kishin Islama.