
Gwamnatin tarayya ta umarci karamin ministan tsaro, Bello Matawalle da shugabannin soji da su koma jihar Sokoto don kawo karshen ayyukan ‘yan bindiga a yankin Arewa maso yamma.
Bayanin hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na ma’aikatar tsaro, Mista Henshaw Ogubike ya fitar.
Umarnin, acewar gwamnatin na daga cikin kokarin da ake yi na kakkabe ayyukan ‘yan fashin daji da masu garkuwa da mutane a Arewa maso yamma.
Gwamnatin ta tarayya ta bayyana bacin ranta kan ayyukan ‘yan bindiga a jihohin inda tayi bayanin cewa matakan da ake dauka ya nuna a shirye ake wajen kawo karshen matsalar.
Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya ce a yayin da zasu kasance a Sokoto, zasu sanya idanu kan ayyukan kawar da Bello Turji da mambobinsa.
“Wadannan ‘yan fashin dajin, suna yada bidiyo na motar sulke ta sojoji da aka ajiye a wajen tabo na ruwa.
” Bayan an umarci jami’an dake wurin su bar wurin saboda gudun kar a farmake su. Amma ‘yan bindiga suka cikin dare suka je yankin suka dau bidiyo da motar suna yadawa suna murna.
“Wannan lamarin ya faru ne a Kwashabawa a karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.
“Baza a amince da hakan ba, a yayin da shugaban kasa Tinubu ya bada goyan baya ga rundunar sojin Nijeriya”, inji sanarwar.