Home Siyasa Ba na tare da Wike a kan cire Ayu — Gwamna Ortom

Ba na tare da Wike a kan cire Ayu — Gwamna Ortom

0
Ba na tare da Wike a kan cire Ayu — Gwamna Ortom

 

 

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya musanta rahotannin da ke cewa yana goyon bayan tsige shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dr Iyorchia Ayu daga mukaminsa, inda ya ce babu yadda za a yi ya goyi bayan cire wanda ya taimaka aka nada.

Jaridar TheCable ta rawaito cewa Ortom din ya kuma ce yana da yakini Mr Ayu zai jagoranci jam’iyyar ga nasara a zaben badi.

Wadannan kalaman sun ci karo da matakin da bangaren Gwamna Wike wanda Ortom mambe ne, da ke neman lallai sai an cire Iyorchia Ayu matukar ana son zaman lafiya a jam’iyyar PDP mai adawa.

Martanin gwamnan na zuwa ne bayan da wata kungiyar ci gaba a jihar Binuwe, Jemgbagh Development Association ta yi zargin cewa Gwamna Ortom na shirya kutungwilar cire dan uwansa na jihar Binuwae wato Mr Ayu.

Kawunan ‘yan PDP sun rabu, tun bayan da aka zabi Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa, inda bangaren Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike yake ta gindaya sharudda daban-daban idan har ana son ya ba da goyon baya a zaben da ke tafe a Najeriya cikin shekara mai zuwa.