Home Labarai Taron APC: Ƴan sanda sun harba wa ƴan jarida barkonon tsohuwa

Taron APC: Ƴan sanda sun harba wa ƴan jarida barkonon tsohuwa

0
Taron APC: Ƴan sanda sun harba wa ƴan jarida barkonon tsohuwa

 

 

 

Jami’an ƴan sanda sun harba wa ƴan jarida barkonon tsohuwa a wajen babban taron APC na ƙasa a Abuja, lamarin da ya tilasta wa mutane guduwa neman mafaka.

Daily Trust ta rawaito cewa tun safe ƴan jarida ke dakon takardar shedar sahalewa su shiga wajen taron, wato Eagle Square don gudanar da aikin su na ɗakko labarai daga kwamitin midiya na taron karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Sule.

Tun mako biyu kafin zuwan wannan rana, gidan jaridu suka kammala shirye-shirye tare da ware ma’aikatan da zasu tura don aikin nemo labarai a wurin taron.