
Daga Hassan Y.A. Malik
An gurfanar da wani dan sanda mai mukamin sajan mai shekaru 29 da haihuwa da aka bayyana sunansa da Sylvester Shamaki a gaban kotun majistare mai zamanta a Yaba, jihar Legas bisa laifin cin zarafin wata budurwa mai shekaru 22.
Mai shigar da kara, Sajan Modupe Olaluwoye, ya bayyanawa kotu cewa, wanda ake zargi ya aikata laifin ne a ranar 14 ga watan Maris, 2018 da misalin karfe 6:30 na yamma a gida mai lamba 9, titin Adebisi Tolani da ke rukunin gidaje na Medina da ke unguwar Gbagada, jihar Legas.
Mai shigar da kara ya ci gaba da cewa, wanda a ke kara ya tilasta kansa akan yarinya da aka boye sunanta ta hanyar gwada karfinsa akanta tare kuma da turbuda dan yatsansa a cikin matancinta.
Wannan laifi ya saba dokar laifuka taa shekarar 2015 ta jihar Legas sashe na 261, inji mai shigar da kara, Olaluwoye.
Sai dai Sajan Sylvester Shamaki ya ki yarda da laifin da a ke zarginsa da shi.
Mai shari’a Misis O.J Oghere, a yayin da ta ke yanke hukunci ta umarci kotu da ta tasa keyar Sajan Sylvester zuwa gidan maza tare kuma da aikewa da kundin karar zuwa ga hukumar kare hakkin bil’adama ta jihar Legas don samun shawarar yadda za ta zartar da hukunci.
Mai shari’a ta dage sauraren karar zuwa ranar 26 ga watan Mayu, 2018.