Home Labarai An taso ƙeyar wasu ‘yan Najeriya 161 daga ƙasar Libiya

An taso ƙeyar wasu ‘yan Najeriya 161 daga ƙasar Libiya

0
An taso ƙeyar wasu ‘yan Najeriya 161 daga ƙasar Libiya

Kimanin ‘yan Najeriya 161 aka taso ƙeyarsu daga ƙasar Libiya dake Arewacin Afurka zuwa gida Najeriya. Su dai ‘yan Najeriyar na zuwa ƙasar ta Libiya ne akan hanyarsu ta zuwa yankin ƙasashen Turai.

Kamfanin dillancin labaru na Najeriya NAN ya ruwaito cewar jirgi samfurin “Boeing 737” mai lamba 5A-DMG ya sauka a sashen aje kayayyaki na filin jigin saman Murtala Muhammad dake Legas ɗauke da mutum 161 daga Libiya da misalin ƙarfe 7:37 na daren Alhamis dinnan.

Su dai ‘yan Najeriyar da aka taso su zuwa gida, su dawo ne da taimakon kungiyar masu lura da ‘yan gudun hijira ta duniya da kuma kungiyar tarayyar Turai “Eurpean Union”.

Mutanan da aka dawo da su sun hada da mata 78 balagaggu, dakuma yara guda 2, sai kuma maza guda 71 balagaggu, da kuma yara 5 da jarirai maza guda 5 suma.

An mika mutanan ne a hannun shugaban hukamar bayarda agajin gaggawa ta ƙasa NEMA, Mustapha maihajja, wanda wakilin shiyyar yankin kudu maso yamma Suleiman Yakubu ya wakilta.

Wakilin ya shaidawa mutanan cewar, tuni Gwamnatin tarayya tayi nisa da tattaunawa da jihohin da wadannan mutane suka fito domin duba hanyoyin da za’a lura da su da basu kulawa.