Home Kanun Labarai Tawagar majalisar dattawa sun kaiwa Dino Melaye ziyarar dubiya a asibiti

Tawagar majalisar dattawa sun kaiwa Dino Melaye ziyarar dubiya a asibiti

0
Tawagar majalisar dattawa sun kaiwa Dino Melaye ziyarar dubiya a asibiti

Tawagar ‘yan majalisar dattawa, karkashin jagorancin Shugaban majalisar Abubakar Bukola Saraki, sun kaiwa Sanata Dino Melaye ziyarar dubiya a babban asibitin kasa dake Abuja, domin jajanta masa abinda ya faru da shi na fadowa da yayi daga mota inda ya samu raunuka.

A ranar Litinin aka tsare Sanata Dino Melaye a filin sauka da tashin jiragen saman kasa dake Abuja akan hanyarsa ta zuwa kasar Moroko domin yin wani aiki na musamman da Gwamnatin tarayya ta tura shi.