
Da alama cikin magoya bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ya ɗuri ruwa bayan da kocin ƙungiyar, Mikel Arteta ya tabbatar da cewa da alama Thomas Partey ba zai buga sauran kakar wasa ta Arsenal ba.
Dan wasan tsakiya na Gunners ya ji rauni a cinyarsa a wasan da Arsenal ta sha kashi a hannun Crystal Palace da ci 3-0 a ranar 4 ga Afrilu, kuma binciken farko ya nuna cewa ya samu rauni sosai.
Partey ya yi fatan zai iya dawowa kafin wasan karshe na Arsenal a kakar wasa ta bana, amma Arteta ya nuna cewa a yanzu da alama hakan ba zai yiwu ba biyo bayan da za a sake yi masa gwaji a wannan makon.
Da yake magana gabanin muhimmin wasan da Arsenal za ta yi a Southampton ranar Asabar, Arteta duk ya tabbatar da cewa dan wasan tsakiya na fan miliyan 45 ba zai sake buga wasa ba har sai kakar wasa mai zuwa.
Kocin Gunners ya ce “Labarin da muka samu bayan an sake tantancewa bai yi kyau ba.” “Ba ya da kyau sosai [don] kasancewar sa a wannan kakar, amma dole ne mu jira mu gani.
“Yana ƙoƙarin dawowa cikin sauri, amma a halin yanzu ba mu da yaƙini game da hakan.”