Home Kasuwanci Tiamin ya samar da gonar shinkafa ta naira biliyan 18 a Bauchi

Tiamin ya samar da gonar shinkafa ta naira biliyan 18 a Bauchi

0
Tiamin ya samar da gonar shinkafa ta naira biliyan 18 a Bauchi

 

Kamfanin Sarrafa Shinkafa na Tiamin ya samar da katafariyar gonar shinkafa da kuɗinta ya kai naira biliyan 18 a ƙauyen Udubo, Ƙaramar Hukumar Gamawa a Jihar Bauchi.
Babban Manajan kamfanin, Aminu Ahmed ne ya baiyana hakan a ranar Talata a yayin dasa tushen gina rukunin ajujuwa guda biyu masu ɗauke da ajujuwa shida a ƙauyen Begu na ƙaramar hukumar Gamawa.
Ya ce gonar itace gona ta zamani mafi girma a Nijeriya wacce ta kai kadada dubu goma, sannan za ta riƙa samar da shinkafa tan 120,000 a shekara, da ma sauran kayan amfanin gona irin su masara.
Ya baiyana cewa kamfanin ya mallaki gonar halak-malak ta hannun gwamnatin Jihar Bauchi bayan ya biya duk kuɗaɗen caji da ya kamata ya biya.
Babban Manajan ya ƙara da cewa ginin ajujuwan wani ɓangare ne na hidimtawa al’ummar yankin.
Ahmed ya godewa Gwamnan Jihar Bauchi, masarautar Katagum da kuma Hakimin Udubo a bisa goyon bayansu da kuma taimakawa wajen ganin aikin ya tabbata.