Home Siyasa ‘Tinubu ya amince da ɗaukar Musulmi a matsayin mataimakin takara’

‘Tinubu ya amince da ɗaukar Musulmi a matsayin mataimakin takara’

0
‘Tinubu ya amince da ɗaukar Musulmi a matsayin mataimakin takara’

 

 

Rahotanni sun bayyana cewa, Bola Ahmed Tinubu, ɗan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, ya amince da ɗaukar Musulmi a matsayin mataimakin takararsa.

Wata majiya mai ƙarfi a Ƙungiyar Yakin neman zaben Tinubu, wacce ta buƙaci a sakaya sunanta, ta tabbatar wa da NAN hakan a yau Lahadi a Abuja.

Majiyar ta shaida wa NAN cewa Tinubu zai bayyana sunan mataimakin takarar a wannan makon.

A makonnin da suka gabata, an yi ta muhawara a ƙasa kan addinin ƴan takarar shugaban kasa da abokan takararsu.