Home Labarai Tinubu ya bada tallafin N100m ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Kano

Tinubu ya bada tallafin N100m ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Kano

0
Tinubu ya bada tallafin N100m ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Kano

 

Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 100 ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Kano.

Tinubu, wanda ya kai ziyarar kwanaki 2 a Kano, ya bayar da wannan gudummawar ne yayin wata liyafar cin abinci da kungiyar ƴan kasuwa ta Kano ta shirya domin karrama shi.

Ya ce an bayar da tallafin ne domin taimakawa da rage radadin da ambaliyar ruwan ta shafa a kananan hukumomin da abin ya shafa.

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar ta bayyana cewa an samu ambaliyar ruwa a kananan hukumomi 19 cikin 44 na jihar, inda mutane 23 suka mutu, 106 suka jikkata, sannan gidaje 12,919 su ka, lalace yayin da gonaki 14, 496 suka lalace a kananan hukumomin biyar.

Da yake jawabi a wurin liyafar, Tinubu ya yi alkawarin tabbatar da cewa bambance-bambancen Najeriya ya zama tushen wadata ga dukkan zababben shugaban kasa a 2023.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya yi alkawarin sake mayar da masana’antun da ake da su tare da mayar da su a matsayin tushen ci gaban masana’antu da bunkasa ba kawai ga Arewa ko Kano ba har ma da kasa baki daya.

Ya kuma yaba wa Gwamna Abdullahi Ganduje bisa kokarinsa na samar da ababen more rayuwa a jihar, inda ya bayyana gwamnan a matsayin “aboki kuma amintaccen abokin tarayya”.

Ya kuma yi wa ’yan kasuwar alkawarin cewa zai samar da yanayin da za a samu ci gaban kasuwanci a jihar.

Masu jawabai a cikin ’yan kasuwar sun gabatar da tsarinsu ga Tinubu, inda suka yi kira gare shi da ya mayar da hankali kan wutar lantarki saboda an rufe masana’antu da yawa saboda rashin isasshen wutar lantarki.