
Shugaban kasa Bola Tinubu ya aika da sakon ta’aziyya zuwa ga gwamnati da al’ummar jihar Niger bisa hatsarin jirgin ruwa da ya faru a ranar Talata a karamar hukumar Mokwa dake jihar.
Jirgin ruwan wanda rahotanni suka bayyana cewa yana dauke da mutane 300 yawancin su mata da kananan yara yayi hatsari a kogin Gbajibo.
Yayin da aka ceto mutane 150, an kuma samu gawar mutane 25.
A sanarwar da mai bai wa shugaban kasa shawara kan fannin yada labarai, Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya jajantawa iyalan wadanda lamarin ya shafa inda yayi addu’ar Allah ya jikansu.
Shugaban kasar ya kuma bada umarni ga hukumar kula da hanyoyin ruwa ta NIWA da ta binciki musabbabin samun yawaitar hatsarin jirgin ruwa a jihar Niger da ma kasa baki daya.
“Shugaban kasa Tinubu ya godewa ma’aikatan bada agajin gaggawa wadanda suka taimaka wajen gano ragowar mutanen”, inji sanarwar.