Home Labarai Tinubu ya kaddamar da motoci masu amfani da lantarki irinsu na farko a Nijeriya

Tinubu ya kaddamar da motoci masu amfani da lantarki irinsu na farko a Nijeriya

0
Tinubu ya kaddamar da motoci masu amfani da lantarki irinsu na farko a Nijeriya

A yau Litinin ne shugaban kasa, Bola Tinubu a Maiduguri ya kaddamar da motocin haya guda 107, ciki har da motocin haya masu amfani da wutar lantarki guda 50 da gwamnatin Borno ta saya.

Da yake jawabi a wajen bikin, Shugaban ya yaba wa Gwamna Babagana Zulum bisa hangen nesa da kuma manufofinsa da ayyukan raya al’umma.

Ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na shirin kafa wata masana’anta ta wannan hanya domin samar da ayyukan yi da kuma saukaka harkokin sufuri.

Tun da fari, Gwamna Zulum ya ce ya fara aiwatar da da shugaban kasa ya bai wa gwamnoni bayan cire tallafin mai.

Ya ce tura motocin haya guda 50 masu amfani da wutar lantarki shi ne irinsa na farko a Najeriya kuma ya yi daidai da hakikanin sauyin yanayi.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa, ya rawaito cewa motocin da shugaban kasar ya kaddamar sun hada da motocin haya masu amfani da wutar lantarki guda 50, motocin bas Coaster 35, motocin Bus Hummer guda 12 da manyan motocin alfarma guda 10.

NAN ya kuma ruwaito cewa shugaban kasar, wanda yake Maiduguri a ziyarar aikinsa ta farko a jihar, ya ziyarci Shehun Borno, Abubakar El-Kanemi.

Shugaban ya kuma bude taron hafsan hafsoshin sojin kasar na shekara.