Home Siyasa Tinubu ya na Landan domin ya huta, in ji mamba a kwamitin yaƙin neman zaɓensa

Tinubu ya na Landan domin ya huta, in ji mamba a kwamitin yaƙin neman zaɓensa

0
Tinubu ya na Landan domin ya huta, in ji mamba a kwamitin yaƙin neman zaɓensa

 

 

Wani mamba kwamitin yaƙin zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Ayo Oyalowo, ya kare ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Bola Tinubu, kan rashin halartar sa hannun yarjejeniyar zaman lafiya da aka kammala.

Da yake magana a gidan talabijin na Arise TV, Oyalowo, wanda ke cikin kwamitin yada labarai na yakin neman zaben, ya yi watsi da rade-radin cewa Tinubu ba shi da lafiya ne.

A cewarsa, ɗan takarar jam’iyyar APC ya na hutawa ne a Landan, inda ya kara da cewa yana cikin koshin lafiya amma ya ɗauki lokaci domin ya huta kafin ƙaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar a hukumance.

Jigon na jam’iyyar APC ya ce bayan ya yi aiki na tsawon sa’o’i 20 a rana, wasu makusantan tsohon gwamnan jihar Legas ɗin sun ba shi shawarar ya huta a kasar waje.

Ya ce: “Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yana Landan. Ba zai iya hutawa a Legas ba, ba za su bar shi ya huta ba. Yawancin lokaci yakan zo Abuja, kuma har nan ma ba za su bar shi ya huta ba.

“Wannan mutumin yana aiki kusan na sa’o’i 20 a cikin sa’o’i 24 a kowace rana. Don haka mutane masu hankali sun ga ya kamata ya bar ƙasar saboda mutane ba za su bar shi ya huta ba tunda yakin neman zabe na nan ba da daɗewa ba,” inji shi.

Oyalomo ya kara da cewa, Tinubu ya riga ya bar kasar kafin gayyatar da hannun zaman lafiya ta zo masa.