Home Labarai Tinubu ya nada manyan daraktocin tashar talabijin ta NTA

Tinubu ya nada manyan daraktocin tashar talabijin ta NTA

0
Tinubu ya nada manyan daraktocin tashar talabijin ta NTA

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada daraktoci bakwai na tashar talabijin ta kasa NTA.

Bayanin hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasar shawara kan fannin yada labarai, Bayo Onanuga ya fitar a yau Juma’a.

Sanarwar ta ce wadanda aka nada din sun hada da:

1 . Ayo Adewuyi – an kara nada shi a matsayin daraktan labarai.

2 . Barista Ibrahim Aliyu – Darakta a fannin ayyuka na mussaman.

3 . Malam Muhammad Fatuhy Mustapha – Daraktan Mulki da bada horo

4 . Misis Apinke Effiong – Daraktan kudi.

5 . Misis Tari Taylaur – Daraktan shirye-shirye.

6 . Mista Sadique Musa Omeiza – Daraktan a fannin kere-kere da kula da na’urori.

7 . Misis Oluwakemi Fashina – Daraktan sashin kasuwanci.