Home Siyasa Tinubu ya buɗe ofishin kamfen a Kano

Tinubu ya buɗe ofishin kamfen a Kano

0
Tinubu ya buɗe ofishin kamfen a Kano
Bola Ahmed Tinubu, ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya buɗe ofishin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar a birnin Kano.
Da yake buɗe da ofishin a jiya Asabar a Kano, Tinubu ya nuna farin ciki da ofishin, inda ya  kuma ya bayyana fatansa cewa APC za ta yi nasara a dukkan matakai a babban zaben 2023 mai zuwa.
“Na gamsu da abin da na gani game da shirye-shirye da kungiyoyin tsarin yakin neman zabe a nan,” in ji shi.
Tinubu ya ce ba wai ya je Kano  don yakin neman zabe ba, sai dai ya je ne domin ya bude ofishin yakin neman zabe da kuma duba yadda aka tsara shi.
Dan takarar na jam’iyyar APC ya tabbatar da cewa idan har aka zabe shi a kan karagar mulki, zai ciyar da kasar nan gaba, kuma ‘yan Nijeriya ba za su yi nadamar zaben sa ba.
“Za mu yi amfani da tsintsiya domin tsaftace kasar da kuma baiwa ‘yan Najeriya farin ciki,” in ji shi.
Tun da fari Gwamna Abdullahi Ganduje ya bada tabbacin cewa al’ummar jihar za su kada kuri’a ga jam’iyyar APC kamar yadda suka saba.
“Kano APC ce, APC kuma Kano ce. Don haka mutanenmu suna cikin jirgin APC kuma muna neman goyon bayansu kamar yadda muka saba,” inji shi.
Gwamna Ganduje ya ce Tinubu jagora ne da zai hada kai da kuma ciyar da kasa gaba.