
Shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya rantsar da Kudirat Kekere-Ekun a matsayin babbar mai shari’a ta ƙasa.
Bikin rantsarwar ya gudana ne a babban ɗakin taro na fadar shugaban ƙasa dake birnin tarayya, Abuja a yau Litinin.
Rantsar da Kekere-Ekun a matsayin cikakkiyar alkalin alkalan Nijeriya ya biyo bayan tabbatar da ita da majalisar dattawa tayi a makon da ya gabata.
A watan Agustan da ya gabata, Majalisar Harkokin Shari’a ta kasa (NJC) ta baiwa Shugaba ƙasa Tinubu shawarar naɗa mai Shari’a Kekere-Ekun a matsayin wacce zata gaji tsohon babban jojin Najeriya, Mai Shari’a Olukayode Ariwoola.
Kekere-Ekun ce babbar jojin Najeriya ta 23 kuma mace ta 2 da ta taɓa riƙe wannan mukami.
Maryan Aloma Mukhtar ce mace ta farko wacce ta rike mukamain babbar mai shari’a ta Najeriya tsakanin watan Yulin 2012 da Nuwambar 2014.