Home Labarai Tinubu ya rantsar da sabbin ministoci 45 da ya naɗa

Tinubu ya rantsar da sabbin ministoci 45 da ya naɗa

0
Tinubu ya rantsar da sabbin ministoci 45 da ya naɗa

A yau Litinin ne shugaban kasa Bola Tinubu ya rantsar da sabbin ministoci 45 da ya naɗa.

An yi rantsuwar ne a dakin taro na Banquet na fadar gwamnati a yau Litinin a Abuja.

Da ya ke jawabi a wajen rantsuwar, Tinubu ya dora wa sabbin ministocin nauyin da su cimma burin ‘yan Najeriya na samun wani sabon ci gaban zamantakewa da tattalin arziki.

Ya ce gwamnatin ta zo ne a daidai lokacin da kasar ke bukatar gyara ta kowane fanni.

“Yan Najeriya suna sa ran za su ga canji a ƙasa kamar yadda muka alkawarta musu a lokacin yakin neman zabe. Da rantsar da ku a yau, kun zama ministocin Tarayyar Nijeriya ba ministocin wata jiha ko yanki ba.

“Yan Najeriya suna tsammanin abubuwa da yawa kuma sun cancanci son ganin canje-canje a rayuwarsu. Yanzu kuna cikin jirgin ruwa guda tare da ni kuma suna tsammanin rayuwarsu za ta yi wani sabon salo mai kyau,” in ji shi

Tinubu ya bayyana cewa sabbin ministocin sun wakilci sassa da al’umma daban-daban na kasar kuma an zabo su ne saboda tarihin nasarori da suka samu a fannonin ayyukansu daban-daban.