
Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da ministoci da jami’ai da shugabannin hukumomi tafiye-tafiye zuwa kasashen waje da kudaden gwamnati.
Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ne ya mika wannan umarni a wata wasika da ya aikewa sakataren gwamnatin tarayya, George Akume.
Wasikar ta ambaci “kalubalen tattalin arziki da kuma bukatar tattala kuɗaɗen gwamnati” a matsayin dalilan dakatar da tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje na wucin gadi ta hanyar amfani da kudaden gwamnati.
Tinubu ya ce idan tafiya ta kama, sai jami’in gwamnati ya nemi amincewar shugaban kasa wanda dole ne a nemi izinin makonni biyu gabanin tafiyar da aka tsara.
Wani bangare na wasikar ya ce, “Shugaban ya damu da kashe makudan kuɗaɗe wajen tafiye-tafiye da Ma’aikatu da Hukumomin Gwamnati ke yi, da kuma bukatar ministocin da da shugabannin ma’aikatu su mayar da hankali kan ayyukan da ke gaban su.
“Bisa la’akari da kalubalen tattalin arziki da ake fama da shi a yanzu da kuma bukatar gudanar da harkokin kudi nagari, na rubuto ne domin in sanar da umarnin shugaban kasa na sanya dokar hana fita na wucin gadi ga dukkan jami’an gwamnatin tarayya a kowane mataki na tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje ta amfani dan kudaden jama’a na tsawon watanni uku daga Afrilu 2024.
“Wannan matakin na wucin gadi an yi shi ne da nufin rage kashe kudi wajen tafiyar da gwamnati kuma da nufin rage kashe kudin wajen tafiyar da aikin gwamnati ba tare da naƙasu ba,” in ji wasikar.