
Jagoran Jam’iyar APC na Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya soke biki na musamman na tunawa da ranar haihuwarsa karo na 13 domin jimamin waɗanda harin jirgin ƙasa ya shafa a jiya Litinin.
Jaridar The Nation ta rawaito cewa Tinubu ya sanar da soke bikin ne mintinan kaɗan kafin a soma.
Tinubu ya siffanta harin da bala’i a ƙasa.
Ya ce “na damu matuƙa a kan lamarin kuma abu ne da ya ke bukatar a yi duba na tsanaki,”
An rawaito cewa tuni manyan baƙi su ka hallara a wajen kafin ya sanar da sokewar.