Home Labarai Tinubu ya tafi ƙasar waje domin hutu da kuma aikin Ummara

Tinubu ya tafi ƙasar waje domin hutu da kuma aikin Ummara

0
Tinubu ya tafi ƙasar waje domin hutu da kuma aikin Ummara

Bayan kammala zaɓen 2023, zababben shugaban ƙasar Nijeriya, Asiwaju Bola Tinubu, ya tafi kasar waje domin hutawa da kuma tsara shirinsa na mika mulki gabanin rantsar da shi a ranar 29 ga Mayu, 2023.

Zaɓaɓɓen shugaban kasar ya bar filin tashi da saukar jiragen sama na Murtala Mohammed dake Ikeja zuwa nahiyar Turai a ranar Talata da daddare.

Zababben shugaban kasar ya yanke shawarar ya huta ne bayan kammala yakin neman zabe, inda zai huta a Paris da Landan, inda da ga bisani ya wuce zuwa Saudiyya domin aikin Umrah da gudanar da azumin watan Ramadana da ya fara a yau Alhamis.

A tafiyar ta sa, Tinubu zai kuma yi amfani da damar wajen tsara shirinsa na karbar mulki.

Ana sa ran zai dawo gida Nijeriya nan ba da jimawa ba.

“Muna kira ga kafafen yada labarai da su daina yaɗa jita-jita da maganganun da ba su da tushe balle makama, sannan su rika neman karin haske daga ofishinmu.” In ji wata sanarwa da ofishin Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasar ya fitar ga manema labarai a jiya Laraba.