Home Labarai Tinubu ya taya al’ummar Musulmi murnar Maulidin Ma’aiki

Tinubu ya taya al’ummar Musulmi murnar Maulidin Ma’aiki

0
Tinubu ya taya al’ummar Musulmi murnar Maulidin Ma’aiki

Shugaban kasa Bola Tinubu ya aika da sakon taya murna da fatan alkhairi ga al’ummar Musulman Nijeriya a ya yin da ake bikin murnar Maulidin Annabi MUHAMMAD (S.A.W)

Shugaban kasar ya yi kira ga Musulmai da su yi amfani da lokacin wajen koyi da halayen Fiyayyen Halitta.

Bayanin hakan na dauke ne cikin wata sanarwar da mai taimakawa shugaban kasar kan fannin yada labarai, Bayo Onanuga ya fitar a yau Lahadi.

“A yayin da muke bikin Maulidi, yakamata mu yi koyi da rayuwar Annabi Muhammad S.A. W da dabi’un sa na tausayi da jin kai”, dole ne mu yi koyi da wadannan halaye na kwarai”, inji shi.

Shugaban kasa Tinubu ya kuma yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi amfani da lokacin hutun Maulidin wajen yiwa kasa addu’a da nuna kauna da jin kai ga kowa.