
Abubakar Sadiq, Kansila mai wakiltar mazaɓar Saminaka a Ƙaramar Hukumar Lere a Jihar Kaduna, ya naɗa masu bashi shawara har guda 32.
Tuni dai takarda mai ɗauke da sunayen masu riƙe da mukaman da kuma ɓangarorin da za su jagoranta ta karaɗe kafofin sadarwa na zamani.
Sai dai kuma da ya ke zanta wa da jaridar DAILY NIGERIAN, Kansilan ya ce ya naɗa waɗannan ɗumbin muƙamai ne domin ya rama alheri da alheri.
A cewar sa, duk waɗanda ya naɗa ɗin, su ne su ka tsaya tsayin-daka har sai da ya samu nasara, shi ya sa shima ya saka musu da irin soyayyar da su ke nuna masa.
Sadiq, wanda shine shugaban masu rinjaye na majalisar Ƙaramar Hukumar, ya ce biyan waɗannan ɗumbin ma’aikata nasa ba abu ba ne mai wahala domin tuni ya tanadi albashinsu da walwalarsu.