
A wani yanayi da ba a taɓa ganin irin shi a Jamhuriyar Nijer ba, masu shagunan sayar da magunguna, wanda a ke kira farmase da yaren faransanci sun tafi yajin aiki.
Tuni dai al’ummar ƙasar su ka fara shiga halin ƙaƙanikayi bayan da masu shagunan magungunan su ka saƙala kwaɗo a ƙyamaren shagunan su sakamakon ƙarin haraji da gwamnatin ƙasar ta yi musu.
Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa masu sayar da maganin sun baiyana cewa ƙarin kuɗin harajin ya yi yawa har ta kai ga ba za su iya jurewa ba, shi ya sa su ka yanke hukuncin garƙame shagunan nasu in yaso kowa ma ya huta.