Home Labarai Titunan Nijeriya duk sun mutu, in ji FERMA

Titunan Nijeriya duk sun mutu, in ji FERMA

0
Titunan Nijeriya duk sun mutu, in ji FERMA

 

Hukumar Kula da Hanyoyin Najeriya ta ce, akasarin hanyoyin kasar da ake kallon su a matsayin tarkon mutuwa, duk sun zarta wa’adin ingancinsu kuma suna bukatar kulawar gaggawa.

Gidan rediyon Rfi ya rawaito cewa Shugaban Hukumar ta FERMA, Nuruddeen Rafin-dadai, shi ne ya bayyana haka a yayin gabatar da wata Makala a birnin Kaduna.

Shugaban na FERMA ya bukaci direbobin kasar da su yi takaa-tsan-tsan a yayin tukin motocinsu a kan manyan haanyoyin kasar saboda yadda suka mutu.

‘Yan Nijeriya da dama ne ke rasa rayukansu sakamakon hadurran ababen hawa a kan hanyoyin da ke sassan kasar.