Home Labarai Tsabagen son rai ne a ce Buhari bai yi aiki a Nijeriya ba — MURIC

Tsabagen son rai ne a ce Buhari bai yi aiki a Nijeriya ba — MURIC

0
Tsabagen son rai ne a ce Buhari bai yi aiki a Nijeriya ba — MURIC

Kungiyar kare hakkin musulmai ta ƙasa, MURIC, ta ce babu wanda ya isa ya kushe kyawawan ayyukan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

MURIC ta bayyana Buhari a matsayin wanda ya yi fice a tsakanin dukkanin shugabannin Najeriya da suka shude.

Farfesa Ishaq Akintola, Babban Daraktan MURIC ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Alhamis a Abuja.

“Mu a kungiyance a ko da yaushe muna al’ajabi abin idan wasu suka yi kokarin lalata nasarorin da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu. Ya yi zarra a tsakanin dukkan shugabannin Najeriya da suka shude.

“Bayan firaministan Najeriya na farko, Alhaji Tafawa Balewa, tsohon Sardaunan Sakkwato, Alhaji Ahmadu Bello da tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Muritala Muhammed, babu wani shugaban Najeriya mai kishin kasa, gaskiya, rikon amana da gaskiya da adalci kamar Muhammadu Buhari.

“Wadanda ke bayyana Buhari a matsayin wanda ya lalata kasar nan, ko dai don rai ne na siyasa ko kuma suna fama da cutar kiyayya da hassada.

“Idan aka yi la’akari da yanayin da ake ciki, Buhari ya samu nasarori da dama ga Najeriya ta ɓangarori daban-daban da su ka hada da tsaro, tattalin arziki, kayan more rayuwa da sauran su,” inji Mista Akintola.