
Gwamnatin tarayya ta ce tashin farashin kayan abinci, man fetur, dizel da sauran kayayyaki ya zama ruwan dare gama duniya, ba wai kawai wata ƙasa guda ɗaya ba.
Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a yau Litinin a Abuja, ya kara da cewa taƙaita matsalar ga Najeriya kaɗai to ya zama yarfe da tsabagen yaɗa kalaman ƙarya.
Ya ce ƙididdiga da ƴan adawa da wani ɓangare na kafafen yaɗa labarai da su ke kwatanta farashin wasu kayan abinci, man fetur, dizel, kafin shekarar 2015 da kuma a halin yanzu, yarfe ne kawai.
“Wannan lissafin domin rano da kididdiga ba gaskiya bane. Waɗanda su ke amfani da waɗannan ƙididdiga ba tare da sanya su cikin mahallin ba to ba su san ma mai sunkenyi ba .
“Mu dauki farashin kayan abinci da man fetur. A duba shafin Google a ga farashin kayan abinci a wasu ƙasashe, musamman Burtaniya da Amurka, za ku ga cewa yayi tashin gwauron zabi. Ba ma a managar farashin iskar gas ko man fetur, ” in ji shi.
Ministan ya kara da cewa matsalar karancin man fetur da ake fama da ita a fadin kasar nan a ‘yan kwanakin nan ya fara samun sauki, yayin da matakan da gwamnati ta dauka sun fara aiki.
Ministan ya ce matsalar karancin man fetur da ake fama da ita a fadin kasar nan a ƴan kwanakin nan ya fara samun sauki, yayin da matakan da gwamnati ta dauka sun fara aiki.