Home Kasuwanci Tsadar man jirgin sama: Kamfanunuwan jiragen sama za su tsayar da aiki nan da kwanaki 3

Tsadar man jirgin sama: Kamfanunuwan jiragen sama za su tsayar da aiki nan da kwanaki 3

0
Tsadar man jirgin sama: Kamfanunuwan jiragen sama za su tsayar da aiki nan da kwanaki 3

 

Kamfanunuwan jiragen sama sun yi barazanar tsayar da aiki nan da kwanaki uku idan har ba a rage farashin man jirgin sama, wanda a ka fi sani da Jet-A1 ba.

Sun kuma yi kira ga Kamfanin Mai na Ƙasa, NNPC, da ya basu lasisinsu fita su kawo man da kan su domin daƙile tsayar da aikin na su.

Shugaban kamfanin jirgi na Air Peace, Allen Onyema, shi ne ya baiyana haka a madadin masu kamfanunuwan jiragen sama yayin wani taron jin ƙorafe-ƙorafe da majalisar wakilai ta shirya, ƙarƙashin jagorancin kwamitin wucin-gadi da ke binciken matsalar man jirgin sama da Ahmed Wase, Mataimakin Kakakin Majalisar ya jagoranta.

Onyeama ya zargi ƴan kasuwar da ke sayar da man jirgin sama da kin faɗin gaskiyar farashin da a ke sauke man, inda ya ce idan har ba a dauki ƙwararan matakai, ba mafi kankanta kuɗin tikitin jirgi zai koma N120,000.

A nashi jawabin, Wase ya ce kwamitin zai yi aiki ne da gaskiyar lamari domin amfanin ƴan ƙasa.

Ya kuma caccaki ƴan kasuwar da yin wani zaurance irin na su domin ɓoye gaskiyar lamarin.

A cewar Wase, bayanan da ƴan kasuwar su ka bayar ba na gaskiya ba ne kamar yadda kwamitin ya fuskanta.

A nashi ɓangaren, Shugaban NNPC, Mele Kyari ya ce kamfanin zai duba yiwuwar baiwa masu kamfanunuwan jiragen sama kasisin shigo da man kamar yadda su ka bukata.

Kyari ya kuma amince da a riƙa sayar da man Jirgin kan N500 lita ɗaya a maimakon N670.