
Wasu manoman masara a jihar Kano sun koma noman dawa ta ƙarfi da yaji saboda tsadar taki, maimakon masara da sauran amfanin gona.
A cewar wani rahoto da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya fitar, manoman a yanzu su na amfani da taki daga kashin dabbobi da sharar gida domin amfanin gona, da karancin taki.
Kazalika manoman sun koma yin noman gauraye, inda suka shuka dawa da gyada ko wake ko waken soya, domin kara haɓaka ni’imar ƙasa domin samun amfanin gona.
Binciken da NAN ta yi ya nuna cewa buhun taki ya kai kimanin Naira 25,000 zuwa sama, ya danganta da nau’i da nau’in kayan.
Wani manomi mai suna Muhammad Tukur ya ce duk shekara ya kan noma masara, amma a bana sai dawa ya shuka, saboda tsadar taki.
Tukur ya ce hakan zai ba shi damar kashe kudi kadan wajen kula da amfanin gona har zuwa lokacin girbi.
Ya kara da cewa ya yi noman gauraye, inda yake gauraya sauran amfanin gona da waken soya waɗanda ke bukatar taki kadan.