
Kotun Tafi-da-gidanka da ta tare da Kwamitin Kar-ta-kwana a kan Tsaftar Muhalli na Jihar Kano ta ci tarar kasuwar ƴankaba Naira dubu 200.
Kotun ta ci tarar kasuwar ne sakamakon ƙin bin dokar tsaftar muhalli ta jihar.
Da ya ke yanke hukunci, Majistare Auwal Yusuf Suleman ya ce an kama kasuwar ne da laifin buɗe wa a cikin awannin hana fita waje sabo da tsaftar muhalli da a ka yi a duk Asabar ɗin ƙarshen wata a jihar.
Wakilin shugaban ƙungiyar ƴan kasuwar, Umar Ibrahim ya riƙe kotun da ta yi musu sassauci bayan ya amsa laifin buɗe kasuwar a lokacin da doka ta hana.
A nashi ɓangaren, Shugaban kwamitin, kuma Kwamishinan Muhalli na jihar, Dakta Kabiru Ibrahim Getso, wanda ya samu wakilci Babban Sakataren ma’aikatar, Adamu Abdu Faragai ya yi kira ga al’umma da su riƙa bin doka.
Ya kuma yaba wa kwamitin a bisa jajircewa wajen aikin sa da kuma tabbatar da an bi doka da oda.