
Budurwar mai suna Sha’awa Nasiru, mai kimanin shekaru 20 ta gamu da gamonta ne, sakamakon tsanin kishi da ya harzuka saurayinta wanda dan sanda ne, hart a kai ya bude mata wuta da binduga sakamakon kin amincewa da soyayyarsa da sha’awa tayi.
Lamarin dai ya faru ne a kauyen Gadar Mallam mamman dake kan hanyar Kaduna zuwa Auja. Dan sandan, ya labe ne a lokacin day a hangi sha’awa ta shiga wani gida, yayin da take fitowa ne, ya kira sunanta, tana amsawa, daman ya dana bindugarsa, ya sakar mata harshashai.
Mutanan kauyen, sun ranta a na kare yayin da suka ji harbin buindiga, inda daga bisani dan sanda, ya silale ya gudu ya bar Sha’awa kwance male-male cikin jinni. Daga baya ne, bayan abin ya dan lafa, mutane suka biyo inda suka jiyo harbin dan ganin abin day a faru, inda suka samu Sha’awa cikin jinni.
An garzaya da ita, zuwa asibitin Doka dake jihar Kaduna, amma abin yafi karfinsu, inda suka ce a mika ta zuwa babban asibiti, sai dai hakan bata samu ba sabida yajin aikin da kungiyoyin ma’aikatan lafiya suke yi, ciki kuwahar da asibitin koyarwa dake gwagwalada.
Yayin faruwar wannan al’amari, wata kawar sha’awa mai suna Salamatu Sani ta shaidawa wakilin Daily Nigerian Hausa cewar, “sha’awa ta shaida wanda ya harbeta a lokacin da suka iso wajenta cikin gaggawa, ta shaida musu cewar ‘insfekto ne’ a cewar Salamatu”.
Sai dai kakakin rundunar ‘yan Sanda ta jihar Kaduna, Mukhtar Aliyu yaki amsa kiran wayar wakilin Daily Nigerian Hausa, haka kuma, yaki maido da bayanin sakon tes da wakilinmu ya aike masa akan wannan batu.